Ali Jita Ya Saki Sabuwar Waka

Photo source : Instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa na salon Nanaye a masana'antar shirye finafinai ta Kannywood dan asalin jahar Kano wato "Ali Isah", wanda ake wa lakabi da "Ali Jita", ya saki sabuwar waka mai suna "Hajara".

Mawaki Ali Jita ya baiyana hakan ne a ranar Alhamis 13 ga watan mayu 2021, wato ranar sallah karama ta bana, a shafin sa na instagram, inda ya tabbatar wa mabiyan sa cewa wakar ya fito tini a manhajojin sauke waka mabanbanta daban daban. Kuma wakar za ta fito ne na salo na daban da yadda aka saba jin wakokin sa na sunayen mata.

Feezy Ya Saki Sabuwar Waka Ta Sallah Tare Da Yan Uwan Sa Biyu.

A cikin shekaran nan da mu ke ciki, mawaki Ali Jita ya fitar da wakoki kuma duk kan su sun kasance a bakin mutane da dama domin kamar yadda aka san mawakin, a fagen soyayya da salon zamani, musanman wakokin sunayen mutane.

A halin yanzu, Ali Jita yana daya daga cikin manyan mawakan Hausa ma su salon Nanaye wanda ake yayin su shekara da shekaru kuma har yanzu ana cigaba da yayin su duk da shekarun da ya yi yana wakokin soyayya daban daban.

Deezell Ya Dawo Nigeria Bikin Sallah.

Leave your comment