Mawaki Queen Zeeshaq Ta Hada Taron Bude Baki Ga Makusantan Ta.

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakiyar Hausa Hip Hop yar asalin jahar Kano, kuma fitacciyar matashiyar ma'aikaciyar radio a Kano Zainab Ishaq wacce aka fi sani da suna "Queen Zeeshaq ", ta hada wa makusantan ta taron bude baki na azumin Ramadan, bayan kwanaki kadan da ta yi rabon kayan abinci ga mabukata da kuma marayu a ranar 26 ga watan Afrilu 2021, wanda ya yi daidai da sha hudu ga watan Ramadan.

Ta yi wannan taron cin abincin ne a ranar juma'a shida ga watan Mayu ta 2021, wanda ranar ne aka kai azumi na ashirin da biyar.

Kundin Waka - Salim Smart Zai fFto Sa Sabuwar Kundin Wakokin Sa

Queen Zeeshaq ta sheda wa wakilin mu da ya halacci wajan taron cewa, dalilin ta na hada wannan taron buda bakin shine, kokarin ta na ganin cewa a sada zumunci tare da kara dankon zumunci a tsakanin juna.

Wanann shine karo na farko da Mace mawaki a masana'antar Hausa Hip Hop za ta hada irin wannan taron buda baki ga masoya ko makusantan ta a a cikin watan azumin Ramadan. Wanda hakan ya janyo hankalin mutane da dama wajan yaba wa kokarin ta akan wannan abu da ta yi, ta shafukan sada zumuncin wadan su ka halarci taron cin abincin.

Sabuwar Waka - Don R Zai Ftar Da Sabuwar Waka.

Zainab Ishaq wato Queen Zeeshaq, ta baiyana wa majiyar mu cewa, ta samu halartar babban aminin ta wato fitaccen mawaki Dabo Daprof wajan wannan taron, kuma ta baiyana farin cikin ta ga maza da matan da su ka samu daman halattan wannan taro.

Leave your comment