Kundin Waka - Salim Smart Zai Fito Sa Sabuwar Kundin Wakokin Sa

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Tin fitowar mawaki Salim, wato bayan fashewar da wakar sa mai taken "Zo mu sasanta" ta yi a wajan mabiya wakokin Hausa na salon Nanaye, Salim smart ya ke cigaba da sakin sababbin wakoki akai akai, sai dai wannan karon, mawakin ya shirya babban tsaraba.

Fitaccen matashin mawaki kuma makadi Salim smart ya sheda wa masoyan sa fitowar sabuwar kundin wakokin sa wacce ya yiwa suna "Muradina" wato a turance (My heart desire), sanarwar da Salim ya yi ta shafin sa na instagram ranar juma'an nan da ta gabata, inda ya tabbatar mu su da cewa, zai fitar da sabuwar waka a ranar sallah karama da za a gudanar a watan Mayu ta shekarar 2021

Daga sunan kundin wakokin, ka na iya nazartar cewa wakokin akan soyayya aka yi su, wanda ya hada da bangaran ta na dadi, daci da kuma rabuwa. Sai dai idan mai karatu ya saurari wakokin ne, sai ya tabbatar da ina wakokin su ka dosa.

Umar M. Shareef Ya Sauya Ranar Sakin Sabuwar Wakar Sa.

Wannan sabuwar kundin ya kunshi wakoki har guda shida (6), wadan da su ka hadar da:

1- Muradina

2- Allah ameen

3- So

4- Ke kadai

5- Sakon Zuciya

6- Na fara so

Idan mai sauraro zai tuna, Salim smart ya saki wakar "Mai kike nufi ne" tare da Fresh Emir a kwanakin bayabayan nan.

Jaruma Maryam Booth Za Ta Yi Karatun Littafi A Gidan Gwamnatin Kogi.

Leave your comment

Top stories