Umar M. Shareef Ya Sauya Ranar Sakin Sabuwar Wakar Sa.

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa na salon Nanaye a masana'antar shirye finafinai ta Kannywood dan asalin jahar Kaduna wato "Umar M. Shareef", ya chanja ranar da ya yi alkawarin fitar da sabuwar wakar sa da fefen bidiyon ta mai suna "Kina Nisa".

Mawaki Umar M. Shareef ya baiyana hakan ne a yau Alhamis 6 ga watan mayu 2021, a shafin sa na instagram bayan shan ruwa na watan azumi da ake, inda ya tabbatar wa mabiyan sa cewa wakar ya fito yanzu haka a shafin sa na YouTube, sabanin yadda ya sanar a da cewa, a ranar jajuben sallah karama ne wakar za ta fito. Kuma wakar za ta fito ne na salo na daban da yadda aka saba ganin wakokin sa.

Jaruma Maryam Booth Za Ta Yi Karatun Littafi A Gidan Gwamnatin Kogi.

A cikin shekaran nan da mu ke ciki, mawaki Umar M. Shareef ya fitar da wakoki da dama kuma duk kan su sun kasance a bakin mutane da dama domin kamar yadda aka san mawakin, a fagen soyayya da salon zamani.

A halin yanzu, Umar M. Shareef yana daya daga cikin manyan mawakan Hausa ma su salon Nanaye wanda ake yayin su shekara da shekaru kuma har yanzu ana cigaba da yayin su duk da shekarun da ya yi yana wakokin soyayya daban daban.

Anyi wannan aikin bidiyon wakan ne a kasar Dubai da ke daular larabawa.

Jaruma Bilkisu Abdullahi Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Ta.

Leave your comment

Top stories