Jaruma Maryam Booth Za Ta Yi Karatun Littafi A Gidan Gwamnatin Kogi.
9 May 2021
Photo credit : Maryam Booth instagram account
By Omar Ayuba Isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Shahararriyar jarumar fim a tagwayan masana'antun shirye finafinai ta Nollywood da Kannywood, yar asalin jahar Kano wato "Maryam Booth" za ta karanta littafi a cikin gidan gwamnatin jahar Kogi da ke a birnin Lokoja.
Jaruma Maryam Booth za ta karanta littafin fitaccen marubuci a Africa dan kabilar inyamurai wato marigayi "Chinue Achebe", mai suna "The problem with Nigeria", a karkashin taron karramawa da za a yi mai suna "Best Nollywood Awards 2021", wanda za a gudanar a ranar yara ta duniya na shekarar 2021.
Jaruma Bilkisu Abdullahi Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Ta.
Za a yi wannan taro ne a ranar 27 ga watan Mayu 2021, da misalin karfe 12 na rana, a cikin gidan Gwamnatin jahar Kogi dake garin Lokoja. Wannan shine karo na farko da jarumar ko wani jarumin daga Kannywood a cikin masu fitowa a finafinan Nollywood zai gabatar da makamanciyar irin wannan abu a gaban mutane a cikin taro.
Maryam Booth, wacce ya ce ga tsohuwar jarumar fim Hajiya Zainab Booth, kuma yaya ce ga matashin jarumi, mawaki kuma makadi Amude Booth, ta fara samun manya manyan dama a cikin finafinan ta na Nollywood, idan ba a manta ba, ko a kwanakin baya ta fito a wani babban fim mai taken "Under Billy", sannan har yanzu Maryam Booth jakadiyar shahararren kwamfanin farin magi na Aji-no-moto ce.
Leave your comment