Jaruma Bilkisu Abdullahi Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwar Ta.

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitacceyar matashiyar jaruma a masana'antar shirya finafinai ta Kannywood wato jaruma "Bilkisu Abdullahi", ta yi bikin zagayowar ranar haihuwar ta a yau Laraba 5 ga watan Mayu 2021.

Da sanyin safiyar yau ne jarumar ta sanar da hakan, bayan da ta wallafa wasu hotunan ta a shafin ta na instagram, inda jarumar ta gode wa Allah da ya raya ta tsawon wadan nan shekarun kuma ta kasance cikin koshin lafiya. Sannan ta nemi masoyan ta da su taya ta murnan ganin wannan ranar.

Latest Songs Hausa: Umar M. Shareef ya saki sabuwar waka.

Bilkisu wacce ta ke cikin jerin jaruma mata ma su mabiya a shafin instagram sama da mutun miliyan daya, ta fito a finafinai da dama wadan da su ka yi tashi.

Kuma jarumar na cigaba da taka rawar gani a cikin masana'antar ta Kannywood. Fim din "Bilkisu", na daya daga cikin fim din da ya kara fito da jaruma Bilkisu a idon ma'abota kallon finafinan Hausa, duba da irin rawar da jarumar ta taka a cikin wannan fim din.

Chizo Germany zai saki sabuwar waka

Leave your comment