Chizo Germany zai saki sabuwar waka

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa Hip Hop dan asalin garin Zaria da ke jahar kaduna,  wanda mazaunnin kasar Germany ne a nahiyar turai, zai saki sabuwar waka daga cikin kundin wakokin sa mai taken "Tsohuwar Budurwa" a cikin makonni ma su zuwa.

Chizo ya sanar da hakan ne ta shafin sa na instagram a daren yau Talata 4 ga watan mayu 2021, inda ya ce wakar za ta fita a ranar 15 ga watan mayu na 2021.

Fefen bidiyon da mawakin ya fitar ya nuna a kasar Germany aka yi wannan aikin, kuma da alama anyi shi ne a yanayin fari da baki wanda aka fi sani da "black and white". Sannan ya baiyana cewa wannan wakar ta daban ce acikin jerin wakokin da ya fitar a yan bayabayan nan.

Chizo Germany na daya daga cikin mawakan Hausa Hip Hop da ke zaune a kasashen turai kuma su ke harkokin su na waka. Ko a Germany din ma, akwai fitattun mawaka irin su "Bello Sisqo", da "Mister Bangis" wanda a kwanakwanan nan ya je kasar.

Leave your comment