Bello Sisqo Zai Saki Sabuwar Waka

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa na salon Nanaye da Afro Pop, dan asalin kasar Najeriya, wanda mazaunnin kasar Germany ne da ke nahiyar turai, zai saki sabuwar waka tare da fefen bidiyo mai taken "Kyakkyawa" a cikin makonni ma su zuwa.

Bello Sisqo, ya sanar da hakan ne ta shafin sa na instagram a yanmacin yau Laraba 5 ga watan mayu 2021, inda ya ce wakar za ta fita a ranar 15 ga watan mayu na 2021, tare da wata baturiyar mawakiya mai suna "Chiara Damico" wacce tare su ka yi wakar.

Ali Jita Ya Ce Real Madrid Daman Sun Gaji Da Daukan Kofi.

Hoton wakar da mawakin ya fitar ya nuna cewa a kasar Germany aka yi wannan aikin, kuma da alama anyi shi ne a salon soyayya, sannan ya baiyana cewa wannan wakar ta daban ce acikin jerin wakokin da ya fitar a yan bayabayan nan.

Bello Sisqo na daya daga cikin mawakan Hausa Hip Hop da ke zaune a kasashen turai kuma su ke harkokin su na waka. Ko a Germany din ma, akwai fitattun mawaka irin su "Chizo 1 Germany", da "Mister Bangis" wanda a kwanakwanan nan ya je kasar.

Umar M. Shareef Ya Sauya Ranar Sakin Sabuwar Wakar Sa.

Leave your comment