Ali Jita Ya Ce Real Madrid Daman Sun Gaji Da Daukan Kofi.

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Daya daga cikin manyan mawakan Hausa na salon Nanaye dan asalin jahar Kano, kuma babban mai goyan bayan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ke kasar spaniya, wato "Ali Isah Jiya", ya baiyana cewa kungiyar sa ta Real Madrid daman ta gaji da daukin kafuna manya a gasar zakarun nahiyar turai.

Umar M. Shareef Ya Sauya Ranar Sakin Sabuwar Wakar Sa.

Ali Jiya ya sanar da hakan ne a daran jiya Laraba 5 ga watan biyar ta 2021, a shafin sa na instagram, bayan da kungiyar ta sa ta Real Madrid ta yi rashin Nasara a wasan da ta buga da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke kasar ingila. Inda Chelsea ta samu Nasara da ci biyu ba ko daya, a zagaye na biyu a wasan kusa da na karshe, na kofin zakarun turai ta champions league na shekarar 2020/2021 da za a fafata wasan karshe a instanbul ta kasar Turkiya.

Ali Jita a cikin kalamai da ke kama da rarrashin kai, ya ce Real Madrid ta gaji da daukan kofuna kuma yanzu lokaci ya yi da za su baiwa wa su dama su ma su dauka.

 Duk da dai hausawa na cewa, wai "Ba haka aka so ba, kanin miji ya fi miji kyau". Cikin wadan da su ka tsokanin mawakin a cikin martanin su, sun hadar da fitaccen mawakin nan na Hausa Hip Hop Dj Ab, inda ya baiyana wa Ali Jita cewa, ai kungiyar ta sa ta Madari sun zama "Kindirmo".

Jaruma Maryam Booth Za Ta Yi Karatun Littafi A Gidan Gwamnatin Kogi.

Leave your comment

Top stories