Hausa Music: Martino Elcasino Birthday Party

Picture source: Mickey de Viper's Facebook page

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin gambayar zamani dan asalin jahar Adamawa wanda duniya ta sani da suna "Martino Elcasino" da aka fi sani da yaro dan maman patient yayi bikin zagayowar ranar haihuwar sa, a ranar 29 ga watan Afrilu 2021.

Daso Ta Yi Rabon Kayan Abinci Amadadin Aisha Buhari.

Martino Elcasino wanda haifeffen "Jambutu, a Jimaita dake Yola ne na jahar Adamawa", ya yi wannan bikin zagayowar ranar haihuwar sa ne a jahar sa ta haihuwa yayin da daukacin mabiyan sa su ke daura hotunan sa a shafukan su na sadarwar zamani mabanbanta dan taya shi farin ciki tare da adduar dacewa da karin daukaka.

Martino na daga cikin Manyan mawakan Hausa Hip Hop daga jahar Adamawa wadan da tin ashekarun baya aka ga futowar su daga wannan jahar, irin su da su Micky de Viper, Maupeen da dai sauran su.

Mata Irin Su Mansura Isah Ba Su Da Yawa Yanzu

Kuma har yanzu da su jahar ke alfahari a duniyar wakar Hausa Hip Hop. Daga cikin mawakan da su ka daura hoton mawakin sun hada da fitaccen mawaki Mickey de Viper wanda a shafin sa na facebook ya yabawa Martino Elcasino tare da taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Leave your comment

Top stories