Deezell Ya Fitar Da Sabuwar Waka Mara Kida

Picture source : Deezell official instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa Hip Hop mazaunin kasar Amurika kuma dan asalin jahar Kano Deezell, ya saki sabuwar waka mara kida da aka fi sani da "Poem" mai taken "Blessed with love " a yanmacin Talata 27 ga watan Afrilu ta 2021 da mu ke ciki, wacce ta zo daidai da ranar da ake da azumi na 15 a watan Ramadan.

Mawaki Deezell ya sanar da fitowar wakar ta sa ne, jim kadan bayan da ya saka gaza mai farashin naira dubu ashirin ga duk wanda ya chanki sunan sabuwar wakar ta sa mara kida. Bayan nan ne ya saki wani dan guntun fefe daga cikin bidiyon tare da daura ta a shafin sa na instagram inda ya sanar da cewa cikakkiyar ta na kan shafin sa na YouTube.

An Cigaba Da "A Yau" Series Na Fresh Emir

A cikin wannan bidiyo, an gano matar Deezell mai suna "Jeddah", inda aka nuno shi a yanayi na damuwa sakamakon rashin jituwar da ke tsakanin su, sai dai ta fito ne amatsayin jaruma ba wai kawai matar sa ba, kuma hakan ya jawo hankalin mutane da dama, kasancewar sun san Deezell yana yawan nuna wa matar sa kauna a fili kuma sai gashi ya saka ta a cikin fefen bidiyo.

Mawaki Queen Zeeshaq Ta Yi Rabon Kayan Abinci Ga Mabukata

Leave your comment