Jaruma Mommy Gombe ta kara shekara daya

Picture source :Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararriyar jaruma a masana'antar Kannywood Mommy Gombe ta yi bikin zagayowar ranar haihuwar ta a yau talata 20 ga watan afrilu 2020. Ta sanar da hakan ne yau da sanyi safiya a shafin ta na instagram, inda ta daura sabbin hotuna a shafin na ta tare da sakon taya kai murna na wannan rana mai mahimmanci ga jarumar.


Mommy Gombe na kan gaba a cikin jarumai mata da ba a fagen fim su ka fi sanuwa ba, a fannin hawa bidiyon wakoki su ka shahara, musanman irin wakokin da ba na cikin fim ba ne, wato wakokin soyayya.

Jarumar dai an fi sanin ta a cikin wakokin fitaccen mawaki Hamisu Breaker da kuma shima fitaccen mawaki kuma jarumi Garzali Miko. Sai Umar M. Shareef da muma sauran jarumai da ma mawakan da ba na fim ba ne.

Kamar dai kullum, yan uwan ta jarumai maza da mata ne su ke ta taya ta murna da farin ciki tare adduar samun dacewa da ma miji na gari, kasancewa jarumar a halin yanzu ba ta da aure.

Bikin ranar zagayowar jaruma Mommy Gombe ya zo daidai da na shahararren jarumi Sani Danja, wanda shi ma yau talata 20 ga watan afrilu ya ke bikin zagayowar ranar haihuwar sa.

Daga nan dai Mdundo muma muna taya wadan nan fitattun jaruman murnar ganin wannan rana muna kuma taya su fatan alheri.

Fresh Emir ya saki sabuwar bidiyo.

Jarumi Sani Danja ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Leave your comment

Top stories