Jarumi Sani Danja ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Picture source :Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen jarumin fim a masana'antar shirya finafinai ta Kannywood da kuma Nollywood da ke kudancin najeriya wato Sani Danja ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a yau Talata 20 ga watan Afrilu 2021, wacce ta fado a cikin watan azumi na Ramadan din bana.


Jarumin ya wallafa wasu zafafan hotuna ne yau da rana a shafin sa na instagram, tare da taya kan sa murnar ganin wannan rana ta zagayowar ranar haihuwar sa. Yayin da wasu daga cikin jarumai abokan sana'ar sa suma su ka daura hoton Sani Danja a shafukan su dan taya shi murna tare da fatan alheri da cigaba.


Suma mabiyan Sani Danja sun taya shi murna tare da masa fatan alheri a karkashin hotunan da ya wallafa a shafin na sa na instagram. Jarumin wanda a kwanan nan ne su ka fara haska wani fim din su mai dogon zango tare da tsohon amin sa Yakubu Muhammad mai suna "Gidan Danger". Kuma har izuwa yanzu ana cigaba da maganar wannan fim a tsakanin mabiyan finafinan Kannywood.

Aisha Tsamiya ta yi kira akan yan danfara a facebook

Jaruma Daso ta shiga sahun jarumai ma su taimakon Ramadan.

Leave your comment