Aisha Tsamiya ta yi kira akan yan danfara a facebook

Picture source :Iinstagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitacciyar jarumar fim a masana'antar Kannywood kuma matashiyar yar kasuwa a halin yanzu, wato jaruma "Aisha Aliyu Tsamiya" ta sanar wa mabiyan ta da kuma abokan cinikaiyar ta cewa bata taba bude tare da anfani da kafar sadarwa a facebook ba, kuma haka zalika jarumar ta ce ba ta da wani alaka da duk wani shafi a facebook mai dauke da sunan ta.

Maryam Booth za ta sake fitowa a wani sabon fim na yan kudu.

Jarumar a cikin fefen bidiyo da ta daura a shafin ta na instagram, ta sheda wa mabiyan ta cewa ita kafar sadarwa ta instagram kawai ta ke yi sai kuma whatsapp, dan haka duk ma su cewa sun yi siyayye a shafin ta na facebook kuma har sun tura ma ta kudi a chan, to fa ba ita ba ce kuma ba ta da wani masaniya akan hakan.

Wannan ba shi ne karo na farko da yan danfara ke amfani da sunan jarumai a kafafan shadarwa ba dan danfarar mabiya wadan nan jarumai, kuma har yanzu wannan salon bai sauya zani ba.

Umar Big show ya koma waka

Hakan ya sa Aisha Tsamiya ta ke kira ga wadan da su ke da bukatar ma'amalar kasuwanci ko cinikaiya da ita, da su gudu hulda da ita a duk wani shafin ta bayan na instagram, domin ba ita ba ce kuma babu sanin ta a game da wadan nan shafukan.

Dj Ab ya aske gashin sa

Leave your comment