Umar Big show ya koma waka

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin nan mai kwamfanin kayan sawa na zamani a jahohi daban daban a arewacin najeriya dan asalin garin Jos mazaunin Kaduna da Kano, wato Umar Big Show da ake wa lakabi da Akwai Swag, ya koma waka bayan yan watanni da fara fitowa a fim.

Matashin wanda ake ganin kaf Kanyywood a zamanin nan babu wanda ya kai shi sanin kayan sawa da hada jarumai maza da mata dan su yi fitar kece raini, ya saki wata sabuwar waka hade da bidiyon ta mai suna "Sautin Murya", yan satittuka bayan da ya fitar da wata waka a kwanakin baya.

Mai kwashewa ya yi wa charki kyautar mota

A hirar da Umar Big Show su ka taba yi da fitaccen mawaki kuma mai gabatarwa Dabo Daprof, a lokacin da aka yi album launch din Fresh Emir na "A Yau Series ", ya baiyana a cikin wannan hirar cewa a baya ya taba waka amma ya bari saboda yana ganin baida basirar waka sosai. Sai ya koma Kaduna yana bin jarumi Adam A. Zango. Daga bisani kuma ya koma harkar sutura wanda anan ne ya yi suna a masana'antar Kannywood.

Mansura Isah bana ta yi rabon abinci kamar yadda ta saba

Ko da Dabo Daprof ya tambaye shi yana da niyar dawowa waka nan gaba, ya tabbatar mai da cewa kware kuwa yana da niya.

Daga dukkan alamu wannan shine dawowar da Umar Big Show ya yi duniyar waka, kuma ana sa ran zai dawo da sabon salo da ya fi na da.

Rahama Sadau ta yi rabon kayan abinci ga mabukata

Big Show dai shi yake wa nawaka manya a Kannywood irin su Hamisu Breaker, Umar M. Shareef da sauran su zabin sutura idan za su yi bidiyo, hoto ko zuwa taron biki.

Leave your comment