Mai kwashewa ya yi wa charki kyautar mota

 

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mai shirya finafinai a masana'antar Kannywood da aka fi sani da Abdul Amart Mai kwashewa ya yi kyauta mota sabuwa ga daya daga cikin makusantan sa a cikin abokan zama da aka sani da Malam Chalke a ranar daya ga watan Ramadan ta 2021.

Jaruma Hafsat Idris ta yi rabon kayan abinci ga masu karamin karfi.

Chalke ne ya sanar da hakan ta hanyan hotunan motar da ya wallafa a shafin sa na instagram, tare mika godiya ga Allah bisa wannan kyauta da aka masa a cikin watan azumi. Ya kuma yabawa Abdul Amart tare da jinjina masa bisa wannan kyautar, sai kuma ya nemi masoyan sa sa su taya shi murna da godiya ga mai daukan nauyin finafinai Abdul Amart.

Tini jarumai maza da mata da dama su ka fara daura hotunan motar a shafukan su dan taya shi murna bisa wannan karuwa da ya samu ta kyautar mota, inda kuma a bangare guda kuma su ke kara yabawa Mai kwashewa bisa wannan kyauta da ya yi wa Charke.

Rahama Sadau ta yi rabon kayan abinci ga mabukata

Leave your comment