Dj Ab ya aske gashin sa

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Kaduna ya aske gashin sa a cikin farkon makon nan da mu ke ciki ta watan Ramadan.

Mawakin ya wallafa hoton askin na shi ne da kuma fefen bidiyo a shafukan sa na sadarwa, inda ya ke jaddadawa masoyan sa cewa wannan shi ne "Haruna", wato sunan mawakin kenan na yanka.

Da yawa daga cikin masoyan sa sun baiyana mamakin su ganin wannan askin da Dj Ab ya yi babu zato ko tsanmani. Musanman yadda wasun su suke ganin ai mawakin ya ma fi kyan gani da rashin gashin.

Inda kuma wasu mawakan ke tsokanan abokin sana'ar ta su da cewa, ya sha kyau ya zama yaro kuma wai ya na kokarin ya kwace mu su budurwar su saboda irin yadda ya yi kyan gani babu suma akan sa.

Isah Ayagi ya fitar da sabuwar waka

Kawa iyan su dai ba a san dalilin sa na wannan askin ba da yayi, duba da yadda mawakin ya sanu da sumar gayu akan sa wanda ya ke sauyawa salo akai akai.

Wannan shi ne karo na farko da za a ga mawaki Dj Ab babu suma, kuma a cikin wadan da su ke tsokanar na sa akwai mawaki Deezell mazaunin kasar amurika da kanin sa Feezy.

Jaruma Hafsat Idris ta yi rabon kayan abinci ga masu karamin karfi.

Leave your comment