Isah Ayagi ya fitar da sabuwar waka

Picture source : Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa mai salon Nanaye dan asalin jahar Kano "Isah Ayagi" ya saki sabuwar waka mai taken "Nayi Budurwa". Ya sanar da hakan ne a shafin sa na instagram a jiya daya ga watan Ramadan da yayi daidai da 13 ga watan Afrilu 2021.

Mawakin ya yi wa masoyan sa albishi da wannan sabuwar wakar da ya ce ta na kan manhajar sa ta YouTube da kuma Audiomack. Kuma wannan ce wakar da mawakin ya fitar tin bayan da ya saki kundin wakokin sa a watanni da su ka gabata.

Kamilu koko ya hana ni kudin da Rarara ya bashi ya bani -AleeGee

Isah Ayagi, daya ne daga cikin matasan mawaka da su ke lokaci a duniyar mawakan rauji da ake wa lakabi da yan Nanaye. Kuma har yanzu wasu suna ganin kamar shi ya ke takewa Hamisu Breaker a baya wajan sharafi da tarin masoya a halin yanzu, musanman su da su ke sa'annu a waka.

Mawakin na daya daga cikin mawakan salon Nanaye da su ke sha'awar sanya turanci a waka jifajifa kamar a cikin wakar sa ta "Amina" da dai sauran su. Kuma haka zalika Isah Ayagi na cikin matasan mawaka ma su tarin baiwar zance da kalaman Hausa ma su zurfin ma'ana kamar yadda wakokin "Aminu Ala" su ke da kuma "Nura M. Inuwa" shima wakokin sa su ke da irin wadan nan kalamai ma su zurfin ma'ana.

Rahama Sadau da Ali Jita sun nishadantar da mutane a Kano

Leave your comment