Hausa Music: Ahmad Delta ya fitar da sabuwar wakar sa

Picture source: Ahmad Delta official Instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawaki mai tasowa kuma daya daga cikin mawakan da ake yayin su a masana'antar Kannywood ma su salon Nanaye a halin yanzu Ahmad Delta ya fitar da sabuwar wakar sa mai taken "Ki na zuciya ta" a jiya juma'a 19 ga watan Maris 2021.

Wakar "Ki na zuciya ta" kamar yadda mawakin ya baiyana a shafin sa na Instagram, wakar ce da makadi kuma mawakin yabo wato zaky dan yaya ya yi aikin audio din. Kuma ti na mawakin ya sanar da cewa wannan wakar ta na nan akan shafin YouTube kamar saura wakokin sa.

Ya kuma bukaci masoyan sa da su garzaya wannan shafin YouTube da sauraren wakar.

Ahmad Delta a cikin shekaran nan ta 2021 na sahun gaba na matasan mawakan da su ke motsi matuka a masana'antar Kannywood musanman yadda ake ta mass sababbin bidiyo da kuma wakokin finafinai da mawakin ke yi a cikin wannan shekarar.

Jaruman biyu da ke kan gaba a jarumai da su ke da mabiya a shafin Instagram

Haka zalika mawaki Ahmad Delta ya fito a cikin wani sabon fim mai dogon zango da ake dauka a cikin gidan hoton nan na Bello Kano Shots dake cikin Ado bayaro mall a garin Kano. Kuma ko a kwanakin bayayan nan, Ahmad Delta ya fitar da fefen bidiyo din wakar sa mai taken "Rashin Masoyi" da aka dauka a garin Abuja, kuma akwai wasu bidiyo da mawakin ya dauka a garin na Abuja wadan da ba su fito ba tukun kamar yadda mawakin da kuma director Aminu S. Bono wanda shi ke bada umarnin wadan nan wakokin su ka baiyana.

Download Hausa Music: Billy-O ya na shirya fitar da wata wakar hadaka.

Leave your comment