Hausa Music: Umar M. Shareef ya fitar da sabuwar fefen bidiyo

Picture source: FUmar YouTube page

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Mawaki kuma jarumi babba a masana'antar finafinai ta Kannywood Umar M. Shareef ya fitar da sabuwar fefen bidiyan wakar sa mai taken "Lagwada".

Wannan sabuwar bidiyo ta fito ne a yau asabar 20 ga watan Maris 2021 a shafin YouTube na mawaki Umar M Shareef. Wanda ya fito yan kwanaki Kadan bayan fitowar audio din wannan wakar ta " Lagwada".

Download Hausa Music: Billy-O ya na shirya fitar da wata wakar hadaka.

Umar M Shareef, wanda ya fito a cikin finafinai da dana tin bayan fara fim da mawakin ya taka rawa na musanman a wadan nan finafinai da ya fito.

Amma duk da wannan finafinai da mawakin ya maida hankali kan su, hakan bai hana Umar M. Shareef cigaba da fito da sabbin wakoki da fefen bidiyo daban daban ba dan jin dadin masoyan sa kamar yadda ya saba.

Wannan ba shi ne karo na farko da mawakin ya ke yin irin wannan bidiyan mai babban aiki ba, idan za'a tina a cikin shekarar 2019 da ta gabata, mawaki Umar M. Shareef ya yi wasu bidiyo biyu a kasar hadaddiyar daular larabawa ba wato Dubai kenan, inda wakokin su ka janyo wa mawakin karin karbuwa ga mabiyan wakokin hausa na Nanaye.

Mawaki Deezell ya fitar da sabuwar waka


Wannan sabuwar wakar ta "Lagwada", makadin nan kuma mawaki dan Lagos wato Selebobo ne ya yi aikin audio din, yayin da kuma Bash 'em ya yi bidiyan wakar.

Wasu daga cikin manyan mawaka da su ka yi fitowa ta musanman a cikin wakar sun hadar da Dj Ab, Tynkingmaigashi, Amar Umar, Lilin baba da dai sauran su.

 

Leave your comment