DJ AB ya samu mabiya miliyan daya a kan Instagram

Photo credit: DJ AB/Instagram 

By El-Yaqub Isma'il Ibrahim 

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararen mawakin Hip-hop DJ AB ya shiga jerin fitattun mawakan da suke da mabiya miliyan daya a kan shafin sada zumunci na Instagram. 

A yau ne DJ AB ya bayyana hakan bayan da ya rubuta sako a kan shafin domin nuna godiyar sa. DJ AB ya fara harkar waka ne tun yana karami bayan da ya saki wakar sa na farko tare da yan uwan sa karkashin kungiyar YNS (Yaran North Side) da wakar Su Baba Ne. Bayan wannan kuwa, ya saki wakoki da dama karkashin kungiyar YNS da wakoki irin su Ameen da Da So Samu Ne.

Scion da Yangaboii ya gayyace BOC, DJ AB, Sojaboy, Blaqshyne da DijayCinch wurin aikin bidiyon sa

DJ AB ya saki wakoki da dama mai zaman kan sa da wakoki irin su Totally, Bombaman, Kumatu, Babban Yaya, Daban Ne, Lukuti da dai sauran su.

DJ AB haifaffen Kaduna ne wanda aka haifa a ranar 30 ga watan Disamba, 1993. A halin yanzu dai yana karatun sa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, jihar Kaduna.

Leave your comment