Bmeri Aboki ya shammashi Dabo Daprof a bikin sa na cika shekara 11

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan garin legas kuma daya daga mawakan Hausa Hip Hop ma su waka daga wajan arewacin kasan nan "Bmeri Aboki", ya shammaci aminin sa fitaccen mawaki Dabo Daprof a bikin da ya shirya na murnar zagayowar ranar haihuwar sa da kuma bikin cika shekara goma sha daya a masana'antar nishadi.

Ado Gwanja zai saki sabuwar waka da bidiyon ta

wanda ya gudana a ranar Asabar 5 ga watan Uni ta shekarar 2021. Bmeri Aboki ya baro garin legas dan halattar bikin ba tare da Dabo Daprof ya sani ba, sai ganin sa kawai a ka yi a wajan taron ya shugo. Wanda hakan ya bar Dabo Daprof cikin mamaki da baki a bude.

A hirar da wakilin mu ya yi da Dabo Daprof, mawakin ya sheda mana cewa, tin a farko wani abokin sa ya kira shi a waya tare da fada ma sa cewa wane fa ya zo Kano kuma yana kan hanyar zuwa wajan taron sa, amma bai yadda ba ya dauka kawai zoleya ce irin ta sa, sai daga bisani, kawar sa Rukayya Abba Kabara, wacce ita ma ta zo taron daga jahar legas din, ta same shi ta ke sheda mai cewa abokin sa Bmeri fa yana kasa bakin wajan shiga taron.

Mawaki Hazy D-Star zai saki sabuwar waka

Wanda hakan ya kara jefa mawaki Dabo cikin mamaki, inda nan take ya bada umarnin a bar shi ya shigo tare da wadan da duk su ke tare da shi. Dabo Daprof ya yabawa Bmeri Aboki a bisa wannan shadaukarwa da karamci da ya mai a wannan biki na shi.

Wadan da su ka halarci taron da dama ne su ka yabawa Bmeri Aboki bisa wannan abu da ya yi wa abokin sa Dabo Daprof, ana kuma fatan ganin wasu mawakan za su fara shirya irin wannan bikin dan murnanr zagayowar shekarun da su ka fara harkar masana'antar nishadi kamar yadda mawaki Dabo Daprof ya yi a wannan shekarar kuma a karo na farko a tarihin Arewa.

Leave your comment