Mawaki Lsvee ya saki sabuwar kundin wakoki

 Photo credit: DJ Ab instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Kaduna da duniya ta san shi a matsayin "Lsvee" ya saki sabuwar kundin wakokin sa mai taken "Mutumina" a cikin karshen watan Mayu da muka yi bankwana da ita na shekarar 2021. Kundin da ake kira a turanci da "EP" wato (Extended Play), wanda ke nifin kundi mai dauke da wakoki yan kadan.

Mr 442 ya saki sabuwar waka

Mawaki Lsvee ya sanar da hakan ga masoyan sa ta shafin sa na instagram, bayan da ya wallafa hoton wannan kundi da ya fitar mai dauke da wakoki guda hudu kawai a ciki, wanda su ka hada da:

1. Akwai Matsala

2. Dadalma tare da Lil Prince da Abba Sboy

3. Mutumina

4. Kudi a banki tare da Deezell.

Har yanzu ba mu hadu da Mr Eazi ba - DJ Ab

Mawakin ya cigaba da baiyana wa masoyan sa cewa wannan kundin ya na dauke da wakoki ma su nishadantarwa da kuma kayatarwa, wadan da su ke dauke da salon zamani musanman irin wanda ake yayi yanzu.

Leave your comment