Auta MG Boy zai saki sabuwar waka

Photo credit: Auta mg Instagram page 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen matashin mawakin Hausa na zamani mazaunin garin Kaduna Auta mg boy ya fara shirin sakin sabuwar waka a cikin wannan makon da mu da za mu shiga na watan Mayu 2021.

Mawaki Auta ne ya wallafa hoton sa, a shafin sa na instagram ranar Alhamis da yanma, inda ya sheda wa masoyan sa cewa zai fitar da waka mai taken "Kece dai". Inda ya bukaci masoyan sa da ke so ya saki wakar su daga hannun su ta hanyar rubutu akan hoton da ya daura, dan ya san yaushe ya dace ya saki wakar.

AUTA MG BOY Ya Sayi Sabuwar Mota

Mr Auta wanda ya ke cikin jerin matasan mawakan da wakokin su ke cigaba da karbuwa sosai a Arewacin Najariya, ya yi sababbin wakokin da ke tashe a yan kwanakin nan, kuma da dama daga cikin wakokin.

shahararren mawaki Adam A. Zango ne ke hawa kan su a cikin bidiyo, Auta wanda a kwanan nan ya siyi Mota kirar fijo ruwan bulu, na bin bayan mawaka irin su Hamisu Breaker da Umar M. Shareef wajan tarin mabiya ma su jin wakokin su.

Leave your comment