Lil Prince ya fitar da sabuwar waka

Photo source : Lil Prince instagram account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Kaduna, kuma daya daga cikin mawakan dake cikin kunguriyar "Yaron North Side", wato (Y.N.S) Lil Prince ya saki sabuwar waka mai taken "Ja muje", a cikin watan nan na Mayu ta shekarar 2021.

Mawaki Lil Prince ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram, cikin hotunan da ya wallafa, na wannan waka da ya saki, tare da shekada wa masoyan sa cewa wannan sabuwar wakar da ya fitar dauke ya ke da salo mai burjewa kuma na chashewa. Kuma ta fita ne a daidai lokacin da yan kwanaki ya rage mawakin ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa.

Lil Prince ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Mawakin wanda yana daga cikin matasan mawaka da ke tashe a jahar Kaduna a halin yanzu, ya fito a cikin wakoki da dama da su ka yi tashe irin su "2019 Cypher", "Da so sa mu ne" da kuma "Ameen". Kuma a cikin wadan nan wakokin ya yi bajinta matuka sosai.

Mawaki Lil Prince na daga cikin mawakan da su ka fito a cikin wakar da fitaccen mawakin Hausa Hip Hop Deezell zai saki mai taken "Super Story ", wacce ya yi ta tare da mawakan Hausa Hip Hop maza da mata mutun ashirin da biyu (22).

Leave your comment