Hamisu Breaker Ya Fitar Da Sabuwar Video

Photo source : Youtube account 

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa na salon Nanaye daga masana'antar Kannywood wato Hamisu Breaker,  ya saki sabuwar fefen bidiyon wakar sa mai taken "Sai da ke", wacce a kwanakin bayan nan ya saki audio din wakar a kafafan sadarwa mabanbanta na zamani.


Manajan mawakin ne ya sanar da hakan a shafin sa na instagram a yanmacin jiya laraba 19 ga watan Mayu ta 2021. Inda ya sanar cewa wakar na nan tafe a cikin kankanin lokaci, sai kuma kwasan a cikin daran laraban dai wannan wakar aka sake ta a shafin YouTube, wanda hakan ya jawo hankalin mabiya akan wannan sabon aikin da su ke dako tin a kwanaki.

Bidiyon dai, wanda kwarenren daracta wanda ya bada umarnin wakar mawaki Namenj da Hamisu Breaker mai taken "Dama" ya yi aikin, ya fita daban da dukkan nin aiyukan da mawaki Breaker ya taba fitarwa a fanin kwarewar aiki da tsarin labari, kamar yadda wasu masana wakokin Hausa na zamani da su ka kalli wannan bidiyo su ka sheda wa majiyar mu ta Madubi Naija bayan da su ka kalli bidiyon.

Nura M. Inuwa Ya Saki Sabuwar Kundin Wakoki

Leave your comment