Dj Ab Ya Tabbatar Da Waka Tare Da Mr Eazy.

Picture source:Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jahar Kaduna kuma daya daga cikin mawakan da ke lokaci a masana'antar ta Hausa Hip Hop wato "Dj Ab " ya sanar da yin waka tare da babban mawaki a Africa d ke garin Legas, wanda duniya ta fi sani da "Mr Easy".

Mawaki Dj Ab ya baiyana wannan labarin ta shafukan sa na sada zumunta daban daban, tare sheda wa mabiyan sa cewa ya yi waka tare da mawaki Mr Eazy, kuma wakar ba karamar waka bace idan ta fito. Duk da bai banyana ko nan kusa wakar za ta fito ba.

Mr Eazy kamar yadda aka sani tin a shekarun baya, ya ke baiwa Dj Ab gudunmawa a fanni daban daban, musanman tun lokacin da Dj Ab ya burge shi a cikin wakar sa da Ab ya juya ta shekarun baya mai suna "London Town". Inda hakan ya jawo kusanci tsakanin mawakan biyu.

Mr Young K Zai Saki Sabon Fefen Bidiyon.

Ko a kwanakin baya, mawaki Mr Easy ya dauki nauyin yiwa Dj Ab bidiyo ta wakar sa mai taken "Kumatu" Kuma ya baiyana cewa zai sake daukan nauyin wani bidiyon.

Dj Ab na cigaba da samun yabo daga masoya wakokin Hausa Hip Hop a fadin duniya, musanman yadda su ka ce mawakin na kara daga marbatar Hausa Hip Hop a idan duniya ta irin wadan nan wakokin hadakan da yake yi da manyan mawaka daga kudu.

Tynking Maigashi Ya Saki Sabuwar Waka

Leave your comment