Kwamfanin Rarara Zai Fitar da Sabon Fim.

[Photo cred: Instagram - Ahmad Delta]

by Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin siyasa mazaunin jahar Kano dan asalin jahar Katsina "Dauda Kahuru Rarara" a karkashin kwamfanin sa mai suna "Rarara Multimedia" zai fitar da sabon fim mai taken "Gidan Dambe".


Wannan sabon fim da ba su sanar da ranar da zai fito ba, ya na dauke da fitattun jarumai a ciki wadan da su ka hada da Tijjani Asase, Daddy Hikima da dai sauran su. Ya kuma samu bada umarni ni daga fitaccen mai bada unarni Iliyasu Abdulmuminu Tantiri, yayin da Aminu S. Bono ya taimaka ma sa, Ummi Ibro ta dauki nauyin fim din.

Also Read: Matasa: Mawakan Zamani da Mawaka Masu bin Salon Gargajiya


Tin bayan da Rarara ya saka gasar nan ta waka akan kasar Najeriya, wannan shi ne abu na farko da zai fitar a karkashin kwamfanin sa ta Rarara multimedia. ana kuma ganin wannan fim zai taka rawa sosai wajan kara tallata yunkurin Rarara na daga martabar masana'antar fim ta Kannywood.


Za mu cigaba da bibiyar mawakin dan sanin ranar da wannan fim zai fita kuma a ina za'a sake shi dan mu sanar mu ku kai tsaye idan lokacin ya yi.

Leave your comment