Yan Danfarar Yanar Gizo Sun Kwace Instagram Din Adam A. Zango.

[Photo cred: Facebook- Adam Zango's]

by Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawaki, makadi, mai shiryawa kuma fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood dan garin Kaduna "Jarumi Adam A. Zango" ya yi rashin instagram account din sa ga yan danfara a yanar gizo da aka sani da "Hackers".


Jarumin ya yi wannan asarar ne cikin kwanakin nan na watan Afrilu 2021, kuma kawo iyanzu duk wani yunkuri dan dawowa da wannan account ya citira. Har jarumin ya bude sabon instagram account mai suna "Sir Adam A. Zango" a matsayin na wucen gadi kafin ya samu dawowa da tsohon.

Also Read: An Kwace wa Mawakiya Queen Zeeshaq Instagram Account


Babban abun mamaki anan shine ganin yadda tsohon account din na Adam Zango ke dauke da tarin mabiya kimanin mutane miliyan daya da wani abu, kuma account din ya na dauke da shedar nan ta verification daga kwamfanin instagram da kan su, wanda hakan ke tabbatar da cewa babu wanda zai iya kwace ta, amma duk da hakan sai gashi jarumi Adam Zango ya rasa wannan account na sa.


Abun dubawan anan shine, samun shedar mallaka ta verification daga kwamfanin instagram ba kariya ba ne kenan ga duk wani mai account na instagram daman? Ko kuma dai jarumin ya yi wani laifi ne daya saba da ka'idar aiki da manhajar instagram din? Muna cigaba da bibiyan ganin yadda za ta kaya a karshe.

Leave your comment