Garzali Miko ya Saki Sabuwar Bidiyo 'Hakuri'

[Photo cred : Instagram-Sunusi Oscar's]

by Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram


Shahararren mawakin Hausa na salon Nanaye kuma jarumi a masana'antar Kannywood dan asalin jahar Kano "Garzali Miko" ya saki sabuwar waka mai taken "Hakuri" a cikin karshen mako na biyu na watan Afrilu ta 2021.


Fitaccen mai bada umarni a masana'antar daracta sunusi 442 ne ya sanar sa wannan fitowar sabuwar wakar a shafin sa na instagram, wanda ta fito a daidai lokacin da ake azumin watan Ramadan na bana.

Also Read: Jaruma Mommy Gombe ta kara shekara daya

Garzali Miko wanda ya fitar da jerin wakoki da dama a cikin wannan shekarar, kuma a kwanaki ya je wasu aiyukan a jahar legas da ke kudancin kasan nan ya kasance daya daga cikin mawakan da su ka fi kowa fitar da fefen bidiyo a mawakan Kannywood na zamani.


Garzali miko na daga cikin kuma mawakan da ke da tarin mabiya kusan miliyan a shafin instagram, amma har yanzu bai samu shedar nan ta verification ba da shafin instagram ke baiwa masu mabiya da dama mai alamun sa hannu da ke dauke da bulun launi a gaban sunan mutun.

Wannan sabuwar wakar dai mawakin ya yi ta ne da jarumar nan mai tashe a cikin mata ma su hawa kan wakoki a cikin bidiyo mai suna "Rakiya Musa" kuma tini wannan fefen bidiyo ya fito a shafukan YouTube daban daban na Kannywood.

Leave your comment

Top stories

More News