Garzali Miko ya saki sabuwar wakar sa ta "Wacce na ke so".

[Picture source : Instagram - Director Sunusi Oscar 442]

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen jarumi a Kannywood kuma nawakin salon Nanaye Garzali Milo ya saki sabuwar wakar sa mai taken "Wacce na ke so" a cikin makon nan da ta gabata a watan Maris 2021 karkashin mai bada umarni daracta Sunusi Oscar 442 wanda shi ya bada umarnin aikin.

Garzali Miko wanda na daga cikin matasan mawakan da ke gan gaba wajan fitar da fefen bidiyo na wakokin da su ka fi karkata kan soyayya amma a kan kidan rawa da salon chashiya.

Hakan ya sanya wakokin Garzali Miko a kan gaba a gidajan wasan dambe da na gala daban daban a kasar nan, wanda kuma ya ke daga cikin mawaka da su ka fi kowa tara ma su kallon bidiyoyin su a YouTube Channel a Arewacin Najeriya, domin Garzali Miko ya na daga cikin mawaka na farko a samun wadan da su ka kalli fefen bidiyon su sama da mutun miliyan 1 da kuma sama da mutane miliyan 2 a wa su wakokin da mawakin ya fitar.
Za'a saki wannan sabon bidiyon ne a shafukan instagram da dama kamar yadda Daracta Oscar 442 ya sanar a kasan rubutun da ya wallafa a karkashin dan guntun bidiyo da ya daura a instagram.

Leave your comment