Hausa News: Mawaki kuma marubuci Dabo Daprof ya zai fitar da sabuwar waka gobe
24 March 2021

Picture source: YK Designer official Instagram account
By Omar Ayuba isah
Get Free Music Updates and Mixes on Telegram
Shahararren mawaki, marubuci, mai gabatawa a gidajan radiyo, kuma daya daga cikin ma su bada gudunmawa a masana'antar Hausa Hip Hop a jihar Kano wanda aka sani Omar Ayuba Isah (Dabo Daprof) wanda masoyan sa wa su ke mai inkiya da Mister Ladagoma, zai fitar da sabuwar wakar sa mai taken "Ganin Ki" gobe Talata 23, ga watan Maris ta 2021.
Wakar "Ganin Ki" waka ce ta hadaka daga mawakan ma zauna studio daya ta "Vocal Sound Studio" wato Dabo Daprof tare da shugaban kwamfanin na Vocal Sound Studio, da matashin mawaki YK Designer da kuma M Khan yaron Sonikman.
An yi wannan wakar ne a watanni hudu da fitar wakar mawaki Dabo Daprof mai taken "Ta Na So" da ta fita a watan Disamba ta 2020. Kuma mawaki sannan makadin zamani wato Sonikman ya yi aikin wakar.
Mawaki Dabo Daprof ya yi sanarwar fitar wannan waka a gobe ne ta shafin sa na Instagram da Facebook a jiya lahadi da yanma, ya kuma sanar da fitar wannan waka a gidajan radiyo daban daban a jihar Kano da ragowar jihohin Najeriya.

Mawakin wanda ke gabatar da wani sabon shiri yanzu a gidan radiyo Nasara mita 98.5 a zangon Fm, wanda kwamfanin wayan nan ta 9mobile su ka dauki nauyin kawo shirin, sannan a yan kwanakin baya ne mawakin ya rasa yayan sa a hadarin motar a jihar Ogun da ke yankin yarabawa, wanda hakan ya sa mawakin ya dauki tsawon lokaci ba tare da ya yi wani sabon waka ba.
Dabo Daprof wanda ya karanci harkar kudi a makarantar Kano State polytechnic tin shekaru hudu da su ka wuce ya rike matsayin social director a wannan lokacin da mawakin ke dalibi a polytechnic.




Leave your comment