Exclusive DJ Mixes and 100% Ad-Free Music!
An karrama jarumi Ty Shaban a matsayin ma'aikacin gidan TV
27 February 2021

Photo source: Ty Shabanfrom Uniquepikin's Instagram handle)
By Omar Ayuba Isah
Babban jarumi kuma ma'aikacin gidan TV na Arewa24 Ty Shaban ya samu karramawa a matsayin ma'aikacin gidan TV a Arewacin Najeriya daya fi kowa hazaka a shekarar 2020.
Wannan karramawar ta fito ne daga bikin karramawa irin sa na farko a jihar zamfara wanda aka hada dan wani bita akan kasuwanci da sana'ar dogaro da kai tare kuma karramawa wasu daga cikin mutanan da su ka nuna bajinta a fanni daban daban a Arewacin Najeriya.
Jarumin wanda ya ke gabata da wani shiri a gidan TV na Arewa24 mai taken "Dandalin Taurari" ya kasance daya daga cikin mutanan da su ke baiwa mawaka da ma jarumai dama ta cikin shirin dan nuna basirar su a fanni daban daban ciki kuwa har da ma wadan da ba waka ko fim su ke ba.
Jarumin ya wallafa wannan karramawa cikin hotunan da ya dauka a ofishin sa da ke cikin garin Kano inda ku ma ya wallafa kotunan a shafin sa na Instagram. Darurruwan masoyan sa ne su ka masa murna tare da Allah sanya alheri da kuma fatan samun cigaba da ya fi wannan.
Weekly Top 10 songs
Top stories
- CHONSE MEDIA
05 April
- Joro Starr ft. Crayon
06 April




Leave your comment