An yi wa Deezell da matar sa kyauta ranar Valentine.

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Shahararren mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jihar Kano mazaunin kasar America Ibrahim Ahmad Rufa'i, wanda aka fi sani da "Deezell" ya samu kyautar musanman tare da matar sa "Jiddah" a ranar Valentine din shekaran nan, wato 14 ga watan febuberi 2021.

Kyautar wanda mawakin ya daura a shafin sa na Instagram da Twitter har ma da na Facebook, na hotunan sa ne tare da matar sa, na tin farkon soyayyar su har na bayan auran su izuwa na bikin cika shekara biyu da auren na su.

Kyautan da wani kwararren mai dauka tare da sarrafa hoto mai suna "Buz22 tv" ya dauka tare da hada su guri daya cikin hoto kwaya daya, ya samu yabo daga mawakin ne tare da dubban masoyan sa da su ma su ke ta yabon ma'auratan kuma sanannun masoya a shafin sada zumunci.

 

Deezell wanda a kwanan nan ne ya saki sabuwar wakar sa ta hada ka tare da mawaka 15 mai taken "Duk abun da zai faru ya faru", ya kasance mawaki na farko a tarihin masana'antar Hausa Hip Hop da ya ke nuna wa matar sa soyayya a fili kuma akai akai, musanman ta hanyar siyo mata kyaututtuka ma su tsada da kuma ziyarar ba zata daga kasar Amurika da ya sha kawo mata anan Nigeria.

Duk da irin suka da kalubalantan da mawakin ke cigaba da sha daga gun wasu da ke ganin bai dace ba ya dinga nuna hotuna da bidiyon matar sa a kafafan sada zumunci, hakan bai taba hana Deezell nuna wa matar ta sa kauna da yabo a fili ba kamar yadda ita na Jiddah wato matar ta sa ta ke yawan yi ma sa ita ma.

Ko a watan nin baya ma sun je kasar Dubai tare inda ya je har da manajan sa tare da shi ma matar sa, a tafiyar wanda shima fitaccen mawaki Dj Ab wanda aminin Deezell ne ya je shima tare da manajan sa. Mawakin wanda a halin yanzu ya na Nigeria tin bayan da aka bude border kasar Amurika da kuma dage takunkumin tafiye tafiye daga kasashe tin bulluwar cutar corona virus, na cigaba da wallafa hotuna kala kala na shi da matar sa a shafukan sa na sada zumunci.

Za mu cigaba da bibiyan mawakin dan kawo mu ku yanda take guda na da shi da matar sa Jiddah.

Leave your comment