Wakar Cin Amana A Rubuce ta Dan Afaka (A's Mai Waka)

AMSHI
Kin sanya raina yai kunci amana batai dadi haka ba...
Alkawar bai ce haka ba...
A So da Kauna ke na rike ban zaton ki cuta min haka ba.

BAITI
Eh haduwarmu kallon ban sha'awa 'yan'uwa ke wa soyayyarmu da ke,
Iyayenmu halin girma da furucin mutunci sunka rike,
Abokai da kawaye ma inuwarmu sunka zuwa su fake,
Shawarata baki nake,
Ni zatona za ki rike,
Ashe tana bin bayan kunne gareki ba tasiri take ba.

BAITI
Rabbi baya zalunci bai halastawa bayinsa ba,
Shi Munafunci Dodo yakan cinye mai shi a gaba,
Shirye-shiryen aurenmu yayi nisa Sam ban gudu ba,
Ashe ke ba ki dau haka ba,
Idanunki suna a gaba,
Kin biyewa zugar su da rudi ban zaton kiymin haka ba.

BAITI
Shaidan yai yo huduba gareki kin bi kin shiga rudani,
Kin biyewa son rai kinyi yaudara gareni mafi muni,
Cin amanar soyayya kikai yi kin saka ni a alhini,
Zuciyata na radadi,
Kuma sonki ya zam sanadi,
Wanga tonon silili ba za ki so ya kai ga iyaye ba.

BAITI
Ki tuna da iyakokin Rabbi kafin na iyaye ma,
Wata baiwa ko ni'ima Rabbi shi yai mana alfarma,
Gunsa ne za Kiy tuba ZulJalaalu shine mai rahama,
Ni hanya ta zan kama,
Ya Rabbana Sarkin Hikima,
Sauya min da alkhairi ya zam ban dauwama kunci ba.

Rubutawa da Tsarawa;
Dan Afaka (A's Mai Waka)
21/01/2025

Leave your comment