RUBUTACCIYAR WAKAR BA ZAN MANTA DA KE BA

Waka: Bazan manta Dake
Rubutawa: Dan Afaka
Rerawa: A's Mai Waka
Fati K/Mashi
Kida: Muh'd Baana
Date: 09th December, 2024

Opening
Na yaba Qaunar ki Don na San kina mini rana.
AMSHI
Ba zan manta da ke ba,
Kina so na da alkhairi kina sharen hawaye na.

BAITI
A kullum zuciya ta na tunanin inda zan kwana,
Idan har nai butulcin so musamman kin yi min rana,
Haqiqar so ina samu kina jinqai da tausai na,
Biyayya kuma kina yi min musamman kan abokai na,
Da zarar na tuno mutuwa randa zan kulle idanu na,
Qwaqwalwa ta takan rude tunda na San mun yi bankwana.

BAITI
Idan har ilimi shine cikar da Ni ko na dace,
Da samun Wanda zai koyar da 'ya'ya na nagartacce,
Haqiqa na yi dacen samun Masoyi na amintacce,
Sanin sirrin masoyin ka kusanci ne da yarda ce,
A cewar wasu in ka sanar da kowa haka wauta ce,
Sirrina kanka zan tona kai nake so ka gane zance na.

BAITI
Abokaina suna da yawa Akwai babban aboki na,
Dare rana yakan zo min da zance kanki Mai sona,
Tunanin ki ne ya zam baban aboki na dare rana,
Da zarar nai shirin barci yakan buden idanu na,
Ba zan kwanta ba har Asuba haka nan ido na yake kwana,
Kullum ALLAH nake roqo Don ya qaran sonki Mai so na.

BAITI
Idan har Rabbi ya yi nufin da aure ni da kai matuqa,
Ina nan raye soyayya da qauna kanka zan tufka,
Kamar Baiwa da Sarkin ta akala gunka zan miqa,
Na zam Mai addu'a kulum hudubar shaidan ina yaqa,
Cikin dadi da ba dadi haquri shi zan aje mariqa,
ALLAH amsan buqatu na ka cikan burin da ke raina.

BAITI
Ashe dai babu jindadi ga duk Wanda bai da Mai son sa,
Irin son nan da za a yi ma kana nan ko kana nesa,
Idan har wani za ya matso jiki na in na numfasa,
Ana jin zuciya ta na bugun so ko kana nesa,
Kamar kurma makaho nake akan Qaunarki nai nisa,
Batun ji ko gani a aje na yaba Don kin yi min rana.

Leave your comment