NASIHA TA Biyu (003)

HAQURI DA RIBA KADAN YAFI ALBARKA FIYE DA YAWAN RIBA BABU ALBARKA NASIHA

Matsayinka Na Dan Kasuwa Duk Qan Qantar Riba Kayi Haquri Da Ita Ka Karba Sai Allah Ya Sanya Albarka a Cikin Kasuwancinka Ya Kuma Cire Maka Tarin Burika, Amma Idan Kaqi Kake Matsa Al'umma Ta Fuskar Buqatuwarka Zuwa Ga Riba Mai Yawa Sai Allah Ya Buda Maka Kasami Arziqin Kuma Babu Albarka Cikinsa Sannan Bazai Magance Maka Matsalolinka Ba

Ku Saurari Wannan Hadisin !
Manzon Allah s.a.w Yace Cewa (Ya Bani Adam Tafarrak Li Ibadati Amlahu Sadaraqa Ginan Wa Asuddu Faqarak, Fa Illam Taf'al Mala Atu Yadaika Shugulan Wala a Sudda Faqarak) Annabi Yace Allah s.w.t Yace Yakai Dan Adam Katsya Ka Bauta Mini Zan Cika Zuciyarka Da Wadata Kuma Na Toshe Qofofin Talauci, Idan Kuma Kaqi Zan Jarabceka Da Talauci Sannan Na Toshe Qofofin Buqatarka
.
Wato Idan Ka Bautawa Allah Yadda Ya Manzon Allah Ya Koyar Allah Zai Sawaqe Maka Tsadar Rayuwa Misali Idan Allah Ya Baka N10,000 Sai Ya Samaka Buqatar Dubu N7000, Ko N8000 Ko N9000 Sau Ran Buqatar Allah Yace Zan Tare Ma'ana Zai Samaka Wadatar Zuciya Tahanyar Rage Maka Tarin Burika Na Duniya
.
Amma Idan Kaqi Bauta Masa Yadda Annabin Rahama Ya Koyar Sai Allah Ya Baka N50,000 Sai Ya Bude Maka Rikicin N150,000 Tahanyar Samaka Azababben Tarin Burika Na Duniya Kuma N150,000 Baza Ta Biya Maka Buqata Ba Saboda Baka Da Wadatar Zuciya Domin Manzon Allah s.a.w Yace (Innal Gina Ginannas) Lalle Dukkanin Wadata Itace Wadatar Zuciya Meke Kawo Wadatar Zuciyar !

Shine Riqo Da Addini Da Kuma Aiki

Leave your comment