Hamisu Breaker ya saki sabuwar bidiyo tare da Mommy Gombe.

[Image Source : Instagram - Director Sunusi Oscar 442]

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Hamisu Breaker bayan fitowa a sabuwar Namenj, fitaccen mawakin ya saki fefen bidiyon wakar sa mai taken "Yar Arewa" tare da Mommy Gombe a cikin makon nan da mu ka yi bangwana da shi ta watan Maris 2021.


Wannan sanarwar ta fito ne daga wajan babban mai bada umarni a Kannywood Sunusi Oscar 442, a shafin sa na instagram. Inda ya ke ya masoyan Hamisu Breaker albishir da wannan sabuwar wakar ta mawaki Hamisu Breaker.

Yanzu haka wannan wakar tini ta fito a YouTube channel kuma masoya da dama ne su ka samun daman kallon wannan fefen bidiyon wakar Yar Arewa, tare da baiyana ra'ayin su kamar kullum akan wannan wakar.

Hamisu Breaker a cikin shekarar nan ta 2021 ya fitar da fefen bidiyo daban daban kuma hakazalika ya fito a bidiyon wa su mawakan na hadaka irin su wakar Namenj mai taken "Dama" da wakar Gfresh Alameen mai taken "Zainaba". A wadan da kuwa ba a mu su bidiyon ba akwai wakar Ado Gwanja ta "Goma Biyar " da su ka yi tare da Breaker.

Har yanzu dai Hamisu Breaker na cigaba da kasancewa a sahun nanyan mawakan Hausa ma su waka irin salon Nanaye wajan daga martabar wakokin Hausa a idon duniya kamar yadda fitaccen mawaki Diamond Platinumz dan kasar Tanzania ya ke yi da yaran Swahili. Kuma daga dukkan alamu nawakin zai cigaba da kasancewa tauraron da za'a juma ana yayin sa a duniyar mawakan Hausa na Kannywood.

Leave your comment