Za'a Cigaba da haska fin din Gidan Badamasi Kashi na Uku

[Image Source : Instagram - Arewa24]

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren fim mai dogon zango mai taken "Gidan Badamasi" da ake haskawa a tashar telabishan na Arewa24 zai cigaba bayan da ya tsaya a kashi na biyu.


Wannan sanarwar ta fito ne daga shafin Instagram din jarumi kuma mai bada umarni a masana'antar Fim ta Kannywood wato Falalu A. Daurayi. Wanda shi ya tsara labarin Gidan Badamasi kuma ya dauki nauyi tare da bada umarnin wannan Fim mai dogon zango.

Tin bayan da aka fara haska wannan fim ne miliyoyin mutane ke cigaba da tofa albarkacin bakin su akan wanna fim mai labarin burgewa da kuma cike da darasi, musanman yadda ma su kallo ke ganin rayuwar da ake haskawa irin ta zahiri ce da ke faruwa a cikin mutane.


Fitattun yan wasa a cikin wanna fim manyan jarumai ne a Kannywood irin su Falalu A. Daurari, Dan Dolo, Nabaraska, Tijjani Asase, Hadiza Gabon, umma Shehu, Ado Gwanja, Horo Dan Mama da dai sauran su.


Za'a fara haska kashi na uku na Gidan Badamasi kamar yadda majiyar mu ta Madubi Naija ya baiyana a ranar 1 ga watan afirilu ta 2021 a tashar Arewa24, kuma a duk ranakun alhamis da karfe 8 na dare.

Muna dagon ganin yadda wannan sabon zangon zai kayatar cikin irin tsari da salon labarin da aka tsara akan wannan kashi na uku (Season 3).

Leave your comment