Ana cigaba da aikin wani sabon fim mai dogon zango irin sa na farko a Kannywood

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Sanannan gidan daukan hoto a cikin Ado Bayero Mall dake garin Kano da aka sani da suna "Bello Kano Shots", sun fara daukan wani sabon fim mai taken" Gidan Hoto" a cikin sabuwar shekarar nan ta 2021, wanda tini anfara daukan wannan fim din a cikin gidan hoton "Bello Kano Shots" dake Ado Bayero Mall.

Wannan fim ya hada bangarori daban daban na Masana'antar Kannywood da ta Hausa Hip Hop. Inda jarumai da mawaka daban daban ne daga bangarorin biyu za su fito a cikin wannan sabon fim mai dogon zango.

Matashin mai bada umarni YK Designer ne ya jagorantar bada umarnin wannan fim, yayin da shi kuma Saif Asnanic ne ke jagorantan shiryawa, yayin da Al- Amren Abdou Muhd ke tsarawa tare darubuta labarin.

Wannan fim din zai maida hankali ne akan fitowa da kananan jarumai da mawaka daban daban ta hanyar hada su da manyan mawaka a cikin fim din. A halin yanzu ana cigaba da daukan wannan fim din a rana ta uku tare da jarumai maza da mata.
Wasu daga cikin jarumai da ake ganin za su taka rawa a cikin wannan fim din sun hadar da "Ali Nuhu, Hamisu Breaker, Ahamd Delta, Dabo Daprof, Bushkiddo, da kuma sauran su.

Bello Kano wanda shi ne shugaban wannan kwamfanin hoto shi ne ke daukan nauyin wannan fim mai dogon zango kuma irin sa na farko a tarihin finafinan masana'antar Kannywood.

Leave your comment