MUTUWAR FUJU'A A KANNYWOOD

13 Janairu, 2025
Duk da cewa yawancin mutane sun yi amanna da cewa komai daren daÉ—ewa wata rana su, da duk wani mai rai za su mutu amma akan shiga hali na kaÉ—uwa da É—imauta idan wani na kusa ya mutu ba tare da tsammani ko kuma wata alama ba.
Wannan ya sa har yanzu masana'antar Kannywood da masu bibiyar ta ba su fita daga jimamin rasuwar fitaccen mawaƙi, Elmu'az Birniwa ba.
Marigayin ya rasu ne a daren Laraba, 4 ga watan Disamban, kuma ya rasu ya bar mata biyu da yara shida.
Wani abu da ya ja hankalin mutane shi ne irin yadda ya yi rasuwar fuju'a, kasancewar lafiya ƙalau ya je filin wasan ƙwallon ƙafa na shirye-shiryen bikin abokin aikinsa mawaƙi Auta Waziri, amma sai dai aka samu labarin rasuwar sa.
Ba wannan ba ne karo na farko da ake samun irin mutuwar a Kannywood, inda a baya an samu wasu fitattun Æ´an masana'antar da suka yi rasuwar ta farat-É—aya, lamarin da ke girgiza masana'antar tare da jefa ta cikin jimami na tsawon lokaci.
Wannan ya sa BBC ta rairayo wasu daga cikin waÉ—anda suka yi rasuwar fuju'a a masana'antar a baya-bayan nan.
Aminu S. Bono

Aminu S. Bono fitaccen darakta ne a masana'antar Kannywood wanda ya rasu a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamban shekarar 2023.
Marigayin ya yi rasuwar farat-É—aya ne bayan ya dawo daga aiki, inda ya yanke jiki ya faÉ—i a cikin gidansa, sannan jim kaÉ—an aka samu labarin rasuwarsa.
An yi jana'izarsa ranar Talata da misalin ƙarfe 8:00 na safe a unguwar Ɗandago da ke cikin ƙwaryar birnin Kano.
ASALIN HOTON, AMINU S. BONO/FACEBOOK
Nura Mustapha Waye

A safiyar Lahadi, 3 ga watan Yulin 2022 ne aka wayi gari da rasuwar daraktan fim É—in Izzar So, Nura Mustapha Waye.
Shi ma Mustapha an yi ban-kwana da shi lafiya ƙalau a daren Asabar, amma aka wayi gari ranar Lahadi ya rasu.
ASALIN HOTON, NURA MUSTAPHA/FACEBOOK
Saratu Daso

A daren ranar Talata 9 ga Afrilun 2024, wadda ta zo daidai da jajibarin Sallah ne Allah ya yi wa Saratu Gidado , wadda aka fi sani da Daso rasuwa.
An ruwaito cewa lafiya ƙalau ta rabu da iyalan ta a daren, kowa ya je ya kwanta, sannan har ma ma ta yi sahur ɗin azumi, amma da gari ya waye, sai dai aka ɗauko gawar ta a ɗakin ta.
ASALIN HOTON, SARATU GIDADO DASO/FACEBOOK
El-Muaz Birniwa

Fitaccen mawaƙi, El-Mu'az ya rasu ne bayan ya je wasan ƙwallon ƙafa na bikin mawaƙi Auta Waziri.
Rahotanni sun nuna cewa da ji wani iri a jikin sa sai ya fita, amma yana fita sai ya faɗi, kafin a ƙarasa asibiti ya ce ga garin ku.
ASALIN HOTON, INSTAGRAM
Binta Ola Katsina

A ranar Alhamis, 4 ga Oktoban 2023 ne jaruma Binta Ola Katsina ta rasu.
Ita ma ta rasu ne bayan ta kammala shirye-shiryen bikin Mauludi a ranar Laraba, amma aka wayi gari ta rasu.
ASALIN HOTON, FACEBOOK
Abubuwan da suke jawo mutuwar fuju'a

A game da abubuwan da suke jawo mutuwar fuju'a, Dokta Adamu Mohammed, wanda ƙwararren likitan zuciya a Jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto ya ce duk da cewa a zahiri al'umma ba za su ga abin da ya yi sanadiyyar mutuwar wanda ya yi mutuwar fuju'a ba, amma zai iya yiwuwa ta samo asali daga wasu cututtukan da ba su bayyana alamomin su a zahiri ba.
Akasari abubuwan da suka fi haifar da mutuwar fuju'a na alaƙa ne da matsalar gazawar zuciya ko kuma rashin isasshen jini a cikin ƙwaƙwalwa.
A wani bayani da Dokta Adamu ya yi wa BBC a baya, ya ce akwai larurori da dama da suke iya haddasa mutuwar fuju'a.
Ya ce da yawa mutanen da kan fuskanci mutuwar fuju'a a mafi yawan lokaci ba su cika kokawa kan wata rashin lafiya mai tsanani ba.
Wasu kuma kan koka kan fuskantar ciwon ƙirji, ko numfashi sama-sama, ko bugun zuciya da sauri.
Rikicewar bugun zuciya

'Arrhythmias' wani yanayi ne da ke shafar bugun zuciyar ɗan'Adam. A irin wannan yanayi zuciya kan ƙara sauri ko kuma ta riƙa bugawa a hankali sosai.
Bugun zuciyar mutum kan ƙara sauri a lokacin da yake motsa jiki ko kuma ya ragu a wasu lokutan amma idan abin ya tsananta zai iya haifar da babbar matsala.
Abubuwan da kan haifar da mummunan sauyin bugun zuciya sun haɗa da shan miyagun ƙwayoyi, sauyi mai yawa a yawan sanadarin pH a jikin ɗan'adam, da matsalar zuciya mai muni da kuma matsalar saurin bugun zuciya.
Sai dai Dokta Adamu ya ce akwai mutanen da ake haihuwar su da matsalar saurin rikicewar bugun zuciya.
Ya ce "abu kaɗan sai ya sa bugun zuciyar su ya rikice". Ya ƙara da cewa hatta damuwa wadda ba ta taka kara ta karya ba kan iya rikitar da bugun zuciyarsu, inda lamarin ke iya sanya wa zuciya ta ƙame, tare da daina bugawa.
"Da zarar zuciya ta tsaya lokaci guda za a samu mutuwa." in ji shi.
Rashin isar jini zuwa cikin zuciya

'Acute myocardial infraction' a Turance, na faruwa ne a lokacin da aka samu raguwar isar jini zuwa cikin zuciya, wanda kan haifar da ƙarancin iska a cikin zuciya da rage ƙarfin zuciya wajen tura jini ga sassan jiki.
Wannan matsala ce ke haifar da lalacewar sassan zuciya, lalacewa ta dindindin.
Wannan na É—aya daga cikin manyan silar mutuwar fuju'a.
Wasu daga cikin abubuwan da suke haifar da wannan matsala sun haɗa da shan taba, da ciwon sukari, da hawan jini, da ƙibar da ta wuce kima, da rashin motsa jiki, da kaɗuwa da shan miyagun ƙwayoyi.
Bugun jini

'Cerebrovascular accident' wanda akan kira shi da 'Stroke' shi ne lokacin da jini ya kasa isa zuwa cikin wani ɓangare na ƙwaƙwalwa ko dai sanadiyyar toshewar jijiya ko kuma fashewar jijiyar. Wannan yanayi kan sanya wasu daga cikin ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa su mutu.
Rashin samun kulawa cikin gaggawa zai iya haifar da lalacewar ƙwaƙwalwa baki ɗayan ta.
Wasu daga cikin alamun bugun jini sun haÉ—a da jiri, da rashin iya magana da kyau, da rashin fahimtar abin da wasu ke faÉ—a, da rashin gani da kyau da ciwon kai nan take.
Toshewar huhu

Wannan kan samo asali ne daga toshewar jijiya a wani ɓangare na jikin ɗan'Adam, musamman ƙafa, inda gundulmin kan tafi zuwa cikin huhu ya toshe hanyar ficewar jini ta cikin huhu.
Wannan kan haifar da mutuwar ɓangaren huhu da lamarin ya shafa, wanda hakan zai hana huhu ya samar da iska ga sauran sassan jiki.
Hakan na iya yin barazana ga rayuwa matuƙar ba a ɗauki mataki cikin hanzari ba.
Lamarin zai iya tsayar da bugun zuciya ko kuma rikirkita harbawar jini daga cikin zuciya.
Kashi É—aya cikin uku na waÉ—anda ke samun kansu cikin wannan yanayi na mutuwa.
Yadda za a ceci mutum

Duk mutumin da ya gamu da ɗaya da cikin matsalolin da ke janyo mutuwar fuju'a kamar yadda likita ya yi bayani a baya, to ba abin da yake buƙata da ya wuce a garzaya da shi asibiti.
Sai dai kafin kaiwa ga asibiti ko samun likita da zai kula da shi, maras lafiyar na buƙatar kulawar gaggawa ta farfaɗo da aikin zuciyarsa wadda a sau da dama take tsayawa da aiki a yayin da mutum ya samu kansa a wannan yanayi.
A wata zantawa da BBC ta yi da Farfesa Kamilu Musa Ƙaraye, wanda likitan zuciya ne a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano a baya, ya yi bayani kan abin da ya kamata waɗanda ke tare da maras lafiyar su yi domin ganin numfashin mutum ko zuciyarsa ba ta tsaya da aiki ba.
Likitan ya bayyana abin da ake kira a Turance kuma a takaice ''CPR'' (Cardiopulmonary resuscitation), inda wani da ya ke da ƙwarewa da wannan hanya zai riƙa danna ƙirjin maras lafiyar, a-kai-a-kai, domin taimaka wa zuciyar ta ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a kai ga asibiti.

Leave your comment

Top stories