WAKAR AISHA A RUBUCE TA DAN AFAKA (A'S MAI WAKA)
13 January 2025
Waka: Aisha
Rubutawa: Dan Afaka
Rerawa: A's Mai Waka
Kida: Harris Lion
Date: 08th Dec, 2024
***
Ba za na barki ba...
Qaunar ki na jiki na...
Komai wuya da rintsi kina cikin zuciya ta Yaa Aisha.
***
Qauna da So nake Wanda ba iyaka da adani...
Komai ya faru kece..
To kar ki bar ni domin rashin ki zai sa na sha wuya Aisha.
***
In kyau ake bida...
Kyawun hali kama...
Ban ce da 'yar da za ta yi yake ba, Komai cikar diya.
***
Kudu na zagaya...
Arewa na bincika...
Gabas da yamma na rasa 'yar da za ta yi ya Aisha.
***
Da za ki so Ni da na warke
Idan da damuwa kin wanke
Farin ciki nake in naji sunan ki Aisha.
***
Me so yake bida?...
Kulawa da lokaci...
Kowa ya samu Wanda ya bashi ba za ya barshi ba.
***
Qauna ruwan jiki...
So garkuwar jiki...
In dai da So haqiqa Aisha ba zan guje ki ba.
***
In gani Ni da ke...
Zan zama garkuwa...
Na yarda rayuwa ta ta zama fansa ga Aisha.
***
Ni ban ga wani tasiri ba...
Na murmushi idan har ba ke...
Kamar ace duhu ba haske haka zan zama in babu ke muradin raina.
***
Idan So ya zama cuta, haquri zai yi maganin sa wannan batun ban aminta ba.
***
Maganin son ki Aisha...
Shine a bani ke...
In aka bani ke to zuciya za ta wartsake.
***
Ke bara ma na fayyace...
In ba ki soni ba...
In ba a bani ke ba ki tabbata za na haukace.
***
Rintsi da baqar wuya ba za su sa in guje ki ba.
***
Ni ban ga wani tasiri ba...
Na murmushi idan har ba ke...
Kamar ace duhu ba haske haka zan zama in babu ke muradin raina.
***
Idan So ya zama cuta, haquri zai yi Maganin sa wannan batun ban aminta ba.

Leave your comment