Abdul Amat Ya Sake Kyautar Mota

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Babban mai bada umarni a masana'antar shirye finafinai ta Kannywood Abdul Amat wanda ake wa lakabi da Mai kwashewa ya kara kyautar mota ga daya daga cikin makusantan sa kuma shaharrren mawakin Hausa na salon Nanaye :Adamu Nagudu".

Mawakin ne ya sanar da hakan ta shafin sa na instagram a jiya Litinin 3 ga watan mayu 2021, bayan da ya daura hoton motar wacce kirar Honda ce baka, inda ya sanar wa abokan sana'ar sa da kuma tarin masoyan sa wannan abun alheri da ya same shi, tare da neman su taya shi murna da kuma godiya ga Abdul Amat, wanda Adamu Nagudu ya baiyana shi a matsayin jagora a tafiyar su ta "Chanji".

Mawaka irin su Ali Jita, Nazifi Asnanic da sauran su ne su ka taya mawaki Adamu Nagudu murnar samun wannan karuwar, tare da ma sa adduar samun wanda ya fi wannan. Wannan shi ne rabon mota ta biyu da Abdul Amat ya yi a cikin watanni biyu ga makusantan sa, wanda hakan ya janyo ma sa tarin yabo daga mabiya finafinan Hausa.

Leave your comment