Ahmad Delta Zai Saki Sabuwar Bidiyo

Picture source: Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa na salon Nanaye mazaunin Kano, haihuwar jahar Delta dake kudancin Najeriya "Ahmad Delta", zai saki sabuwar fefen bidiyo mai taken "Lubiyar Soyayya" a cikin yan kwanaki ma su zuwa.

Mawaki Ahmad ya sanar da hakan ne a shafin sa na instagram, inda ya sheda wa masoyan sa da cewa wannan waka zai fito nan ba da jumawa ba, kuma za su iya sauke ta a wayoyin su ta manhajoji daban daban idan lokacin ya yi.

Ahmad Delta wanda a kwanakin baya ya fitar da sabuwar wata mai taken "Ruwan Zuma", ya na daya daga cikin matasan mawakan da ake ji da su a masana'antar Kannywood, ake kuma sa ran za su shiga sahun mawaka irin su Hamisu Breaker da Garzali Miko da dai sauran su wadan da a halin yanzu da su ta ke yi kuma su na da tarin masoya a Arewacin kasan nan da ma sauran sassa a duniya.

"Lubiyar Soyayya", waka ce akan soyayya da halin da mai yin ta ke shiga a lokacin da ta juya mai baya. Wanda da wannan salon aka san mawaki Ahmad Delta a cikin mawakan Kannywood ma su tasowa.

Leave your comment