Mawaki Ashraff ya yabi babban makadi Dj Mekku

Picture source : AleeGee's official instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

 

Fitaccen mawakin Hausa kuma makadin zamani na salon Nanaye Nura Ashraff ya yabawa shahararren makadi Mai kudi da aka fi sani da Dj Meku abisa taimakon sa da ya yi a lokacin da ya fara koyan kida da harkar waka.

Mawaki ashraff ya baiyana hakan ne a shafin sa na instagram cikin mawakon da ta gabata ne na watan Maris 2021, inda ya wallafa hoton Dj Meku yayin da a kasan hoton mawakin ya rubuta sakon godiya da dan takaitacciyar labarin abun da Dj Meku ya yi ma sa a rayuwa. A kalaman mawaki Ashraff ya ce:
"Shi (Dj Meku) ne mutun na farko da ya fara yin mun rana a rayuwa ta a yayin da na ke neman madafa a gun aiki. Oga na, mai gida na, aboki na ko kuma na ce amini. Meku production, Allah ya kyautata rayuwar ka ya kara suturta ka. Legend music producer.


Ko da wallafa wannan rubutu da makadi Ashraff ya yi akan Dj Meku, shi ma makadi kuma mawakin Hausa Hip Hop AleeGee ya daura hoton da Ashraff ya saka a nasa shafin instagram din tare da kara jaddada yabo ga makadi Dj Meku wanda mai gida ne ga shi ma AleeGee din. Shi ma shahararren mawakin Hausa Hip Hop kuma fitaccen marubuci Dabo Daprof ya baiyana ta sa yabon a kasan hoton da AleeGee ya wallafa, inda ya baiyana cewa Dj Meku ne mutun na farko da ya fara masa aikin waka a shekaru da dama da su ka wuce, tin shi dj Meku din ya na kida a studio din fitaccen mawaki makadi karmatako.

Haka zalika mawaka da masoya da dama ne su ke ta jaddada yabo ga dj meku tare da fatan alheri a gare shi.

Leave your comment