Yakubu Muhammad ya taya Nabaraska murnar samun karuwa ta haihuwa

Picture source: Yakubu Muhammad official instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawaki, jarumi kuma daya daga cikin shugaban kwamfanin shirya finafinai a Kannywood Yakubu Muhammad ya taya abokin sana'a Mustapha Nabaraska murnar karuwa da ya samu ta haihuwa a makon data gaba ta, jarumin ya taya wannan murnar ne a shafin sa na instagram a ranar sunan jaririyar da jarumi Nabaraska ya sanyawa suna Amina.

Yakubu Muhammad wanda shi ma ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a cikin makon da ya wuce na wannan watar ta Maris 2021 da mu ke ciki, wanda aminin sa Sani Danja da kuma iyalin sa Mansura Isah su ka shirya ma sa dan bikin taya murna tare da yan uwa da abokan arziki, ya kara da yiwa Nabaraska adduar fatan Allah ya raya abun da aka samu da kuma karin zaman lafiya.

Nabaraska wanda daya ne daga cikin fitattun yan barkwanci a cikin finafinan Kannywood, kuma a halin yanzu jarumin na taka mahimmiyar rawa wajan nishadantar da ma su kallon finafinan Hausa, musanman a cikin fim mai dogon zango Gidan Badamasi da ake haskawa a tashar Arewa 24.

Jarumai maza da mata da dama ne su ka taya jarumi Nabaraska farin ciki da adduar Allah raya da na Allah sanya alheri. Mu ma daga nan Mdundo mu na wa jarumi Nabaraska fatan alheri da rokon Allah ya raya yar sa Amina.

Leave your comment