AleeGee da Rarara su na aikin waka tare

Picture sources : official AleeGee's Instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop kuma makadi a masana'antar Hausa Hip Hop din da kuma ta kannywood wato AleeGee, dan asalin jahar Katsina mazaunin jahar Kano ya na aikin wakoki da fitaccen mawakin siyasa Dauda Kahutu da aka fi sani da "Rarara".

Fefen bidiyo da mawakin ya daura yau a shafin sa na instagram ne ya tabbatar da hakan ga masoyan AleeGee "the Hausa rapper" kamar yadda mawakin ke wa kan sa inkiya.

Tin a yan kwanakin baya ne ake ta ganin AleeGee ya na daura fefen bidiyon shi da Rarara a cikin studio su na tare, inda shi AleeGee ke kida shi kuma Rarara ke zaune kusa da shi ko a nuno shi a zaune bayan AleeGee din. Wanda tini masoyan mawaki AleeGee su ka fara baiyana ra'ayoyin su kan wannan sabuwar alakar tsakanin mawakan biyu.


AleeGee dai na daga cikin mawakan da su ka shiga gasar waka da mawaki Rarara ya saka a cikin watan Feburerun 2021 da ta gabata, kuma ana sa ran AleeGee na iya lashe wannan gasa ko ya kasance daya daga cikin mawaka goma na farko a cikin gasar.

An dade ana sa rai da samun kyakkyawar alaka tsakanin mawakan siyasa, mawakan Nanaye da kuma nawakan Hausa Hip Hop, sai dai hakan bai samu ba shekara da shekaru sai a yanzu aka fara gina wannan alakar, kamar yadda aka ga AleeGee tare da Rarara su na aiki, haka shi ma mawaki Hamisu Breaker su ka hadu cikin wani aiki tare da mawakin Hausa Hip Hop Namenj wanda aka san shi a salon Afro beat wato(Afro Pop) kamar yadda aka saba kiran wannan salo. Sun yi sabuwar waka mai suna "Dama" ta Namenj da kuma Ali Jita da su ka yi tare da Dj Ab.

Leave your comment