Ali Nuhu ya yi allurar Corona Virus

Picture source : Ali Nuhu official instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Jigo a masana'antar shirya finafinai kuma fitaccen jarumi kuma mai bada umarni jarumi Ali Nuhu ya yi allurar kariya ta Corona Virus wato Covid 19 a yau alhamis 25 ga watan Maris 2021. Jarumi Ali Nuhu ya sanar da hakan ne ta cikin fefen bidiyo da hotuna da jarumin ya dauka a lokacin da yake karban wannan allurar ta Corona Virus. Inda ya sheda karbar wannan allurar kariyar daga cutar Covid 19 da ke cigaba da addabar Al'umar duniya tin bayan dawowar cutar a karo na biyu kuma a matakin da ya fi na da.


Jarumin ya nuna katin shidar karbar allurar wacce aka rubuta a jikin takardar cewa "Allurar Covid 19 ingantaciya ce kuma mara illa ga jiki". Wannan rubutun tabbacin ba zai rasa nasaba da irin jitajitan da ke yawo akan wannan allurar rigakafin ba a sassa daban daban na duniya tin bayan fitowar allurar.


Kawo yanzu, jarumi Ali Nuhu shi ne mutun na farko a jaruman Kannywood da su ka karbi wannan Allurar ta rigakarin corona virus, sai dai akwai yuwar tasirin jarumin ga wasu jaruman kan sanya su karban wannan allurar rigakafin ta corona virus.

Leave your comment