Jarumi Yakubu Muhammad ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa

Picture source : Yakubu official instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararrren tsohon mawakin salon Nanaye kuma jarumi a tagwayen manana'antar shirya finafinai ta Nollywood dake kudancin Najeriya da Kannywood dake arewacin kasar nan Yakubu Muhammad yayi bikin zagayowar ranar haihuwar sa yau Alhamis 25 ga watan Maris shekarar 2021.

Fitaccen jarumin ya baiyana wannan bikin ne ta shafin sa na instagram inda ya wallafa hotunan sa har kala shida duk dauke da sakon taya kai murnar zagayowar ranar haihuwar sa. Wanda tini darurruwan masoyan sa daga sassa daban daban ne su ke ta aikawa jarumin sakon taya murna da fatan alheri.

Wasu daga cikin manyan cikin manana'antar kannywood da su ka taya jarumin murna a shafukan kan su na sada zumunci sun hadar da babban aminin sa Sani Musa Danja, Saratu Gidado Dasu, Daracta Sunusi442 da sauran su.


Yakubu Muhammad wanda ya shahara a fagen wakokin finafinan Kannywood da kuma a matsayin sa na jarumi kuma daya daga cikin mamallakan kwamfanin shirya finafinai ta 2Effects, ya kasance daya daga cikin jaruman da ake ganin sun juma tauraron su ya na haskawa a masana'antar kuma har yanzu da su ake cigaba da damawa.

Leave your comment