Nabaraska ya samu karuwa ta haihuwa

Picture source : Nabaraska official instagram account

By Omar Ayuba isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren jarumin bargwanci a masana'antar Kannywood Mustspaha da aka fi sani da Nabaraska ya samu karuwar ta haihuwa a ranar juma'a 19 ga watan Maris ta 2021, Inda jarumin ya baiyana cewa Allah ya albarkace shi da haihuwar ya mace cikin sauki ba tare da matsala ayayin haihuwar ba.

Da mahaifiyar da jaririyar duk su na cikin koshin lafiya kamar yadda jarumin ya baiyana ta shafin sa na instagram kamar yadda majiyar mu ta Madubi Naija ya wallafa. Jarumi Nabaraska wanda ke taka rawa a cikin fitaccen shirin fim mai dogon zango na "Gidan Badamasi" da gidan talabijan na Arewa24 ke haskawa tare da daukan nauyin shirin.

Nabaraska wanda ya fito a manya manyan finafinai irin su "Basaja", "Gidan Badamasi" da dai sauran su, ya samu karbuwa ne a wajan nabiya finafinan Kannywood saboda salon barkwancin sa na saka turanci gurbaceciya a cikin zancen sa idan ya na yi. Wanda da wannan salon ne jarumin ya sanu ya kuma karbu a cikin manana'antar fim ta Kannywood.

Daga nan Mdundo kamar ragowar jarumai ma su taya Nabaraska Murna, muna taya shi murna da fatan Allah ya raya.

Leave your comment